Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da makon kirkire-kirkie na Afirka na bana a hedkwatar AU
2019-10-28 20:29:32        cri

A yau Litinin ne, aka kaddamar da makon kirkire-kirkire na Afirka na shekarar 2019 (AIW) a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka (AU) dake Addis Abba, babban birnin kasar Habasha. Makon da ya hallara daruruwna matasa masu basirar kirkire-kirkire daga sassa daban-daban na kasashen Afirka da arewacin Turai da na Atilantika.

A jawabinsa na bude makon, shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya nanata cewa, makon hadin gwiwa ne da shirin raya ajandar kungiyar nan da shekarar 2063, kundin dake kokarin samar da makoma mai haske, hadewa da samar da zaman lafiya a nahiyar nan da shekarar 2063. Kana makon zai samar da tarin damammaki a fannoni daban-daban.

Manufar makon, ita ce samar da nagarcin tsari ga masu tsara manufofi da masu bincike da masana da sassa masu zaman kansu da abokan hulda na kasa da kasa da suka mayar da hankali wajen zurfafa kirkire-kirkire da samar da ci gaba mai dorewa a Afirka.

Yayin makon wanda za a shafe kwanaki 6 ana gudanarwa, za kuma a nuna wasu fannoni da suka kunshi kirkire-kirkiren mata da harkokin kasuwanci, aikin gona da birane na zamani, gidaje da makamashin da ake iya sabuntawa, manyan na'urori, kiwon lafiya, yawon bude ido da masaukai na zamani, da batun cinikayya da zuba jari.

Bugu da kari, a yayin makon, za a nuna ci gaban da aka samu a fannin kirkire-kirkire, da ma irin muhimmin tasirin da bangare ya yi a rayuwar daruruwan miliyoyin 'yan Afirka a fannin kirkire-kirkire da guraben ayyukan yi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China