Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Mauritius sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki maras shinge
2019-10-18 12:34:22        cri

Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta sanar cewa, kasashen Sin da Mauritius sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki maras shinge wato FTA a jiya Alhamis, wannan shi ne karon farko da kasar Sin ta kulla irin wannan yarjejeniya ta FTA tsakaninta da wata kasa ta Afrika.

Yarjejeniyar cinikin tsakanin Sin da Mauritius ita ce yarjejeniyar FTA karo na 17 da kasar Sin da kulla.

Wannan yarjejeniya ta kunshi bangarorin cinikin hajoji, ayyukan hidima, zuba jari, da kuma hadin gwiwar tattalin arziki.

Ita dai yarjejeniyar FTA ba wai za ta samar da karin karfin iko da tabbacin zurfafa mu'amalar bangarorin ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu ba ne, har ma za ta kara karfafa dangantakar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Sin da Afrika, a cewar ma'aikatar kasuwancin kasar Sin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China