Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu ya nemi afuwa bisa hare haren kin jinin baki da ake kaiwa a kasarsa
2019-09-15 15:34:05        cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce kasarsa na aiki tukuru wajen kawo karshen hare-haren kyamar baki da wasu 'yan kasar ke kai wa baki 'yan kasashen waje mazauna kasar.

Da yake jawabi a wajen bikin binne tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a birnin Harare, shugaba Ramaphosa ya ce, 'yan kasarsa ba su kyamar baki, sannan ya nemi afuwar 'yan Zimbabwe da sauran 'yan Afrika, game da hare-haren kyamar baki da suka yi sanadin mutuwar mutane 12, ciki har da 'yan Zimbabwe 2, tare da raba daruruwa da matsugunansu a kasar Afrika ta kudu.

Ya ce, abun da ya faru a Afrika ta kudu ya sabawa ka'idar hadin kai ta al'ummar Afrika, wadda marigayi Mugabe da marigayi tsohon shugaban kasar Nelson Mandela da sauran shugabannin juyin juya hali a nahiyar suka yi rajin tabbatarwa.

Ya kara da cewa, kasarsa na maraba da jama'ar sauran kasashe, kuma za su yi aiki tukuru wajen karfafawa da inganta zaman takewar dukkan al'ummar Afrika ta kudu dake rayuwa da aiki tare da mutanen sauran sassan nahiyar.

Ramaphosa ya yi jawabin ne bayan 'yan kasar Zimbabawe da suka halarci bikin binne tsohon shugaban kasar da aka yi a filin wasanni na kasar, sun nuna rashin jin dadinsu game da hare-haren na kyamar baki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China