Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar kasashen Sahel 5 na neman hada hannu da Rasha kan yaki da ta'addanci
2019-10-25 10:18:10        cri

Mai rikon shugaban kungiyar kasashen Sahel 5, kuma shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, ya nemi hadin gwiwa da Rasha, domin kulla dangantaka mai karfi wajen yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Shugaba Christian Kabore, ya bayyana haka ne cikin jawabin da ya yi a taron kasashen Afrika da Rasha da aka yi a Sochi na Rasha.

Shugaban ya bayyana cewa, yankin yammacin nahiyar Afirka na fuskantar yawaitar hare-haren ta'addanci da suka kai ga mutuwar mutane sama da 500 da raba wasu sama da 450,000 da gidajensu, tun daga shekarar 2015.

Ya ce yana son yin kira ga Rasha, ta kulla dangantaka mai karfi da yankin Sahel ta kuma mara baya ga shirinsu na yaki da ta'addanci.

A watan Satumban da ya gabata ne, yayin wani taron musammam na kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS, da aka yi a birnin Ouagadougo na Burkina Faso, aka amince tare da zartar da wani shiri na tara dala biliyan 1 domin yaki da ta'addanci.

Za a yi amfani da kudin ne wajen samar da kayayyakin tsaron kasa da na rundunonin hadin gwiwa na kasashen ECOWAS mai mambobi 15. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China