Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saurin bunkasuwar biranen Afrika yana janyo hankalin masu zuba jari a nahiyar
2019-10-16 09:43:09        cri

Wani sabon rahoton da aka fitar a Nairobi ya ce, nahiyar Afrika tana samun karuwar kamfanoni dake zuba jari a nahiyar.

Rahoton wanda Cytonn, wani kamfanin zuba jari dake Nairobi ya fitar, ya danganta karuwar kamfanonin masu zuba jarin da ake samu a nahiyar da cewar saurin bunkasuwar birane da ake samu a nahiyar shi ne ya haifar da hakan, lamarin da ke kara samar da al'umma masu matsakaicin matsayin tattalin arziki da kuma karuwa masu sha'awar sayan kayayyaki.

Rahoton ya kara da cewa, hasashe ya nuna cewa, yankin kudu da hamadar Saharar Afrika ya fi samun saurin bunkasuwa idan an kwatanta da kasuwannin duniya.

Kamfanin ya ce, sun himmantu matuka a matsayinsu na kamfanonin zuba jari a shiyyar hamadar Saharar Afrika. Samun karin riba na masu zuba jari da kyakkyawan yanayin tattalin arziki zai ci gaba da bunkasa kasuwannin Afrika.

Kasashen Kenya, Najeriya da Ghana suna daga cikin kasashen dake matukar janyo hankalin kamfanonin zuba jari, a cewar rahoton kamfanin na Cytonn.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China