Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rawar da Sin ke takawa a siyasar duniya ta taimakawa ci gaban Afirka
2019-10-03 15:14:17        cri

Babban mai bincike a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa dake Najeriya (NIIA) Efem Ubi, ya bayyana cewa, muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin siyasa da tattalin arziki na duniya, ta amfanawa galibin kasashen Afirka.

Efen Ubi, ya ce, haka kuma kasar Sin ta kasance kashin bayan harkokin tattalin arziki da siyasar duniya, tana kuma aza harsashin da ya dace, ta hanyar amfani da manufofinta da dangantakar abokantaka ta cin moriyar juna da kasashen Afirka, ta yadda nahiyar za ta samu madogarar bunkasa.

Ubi, ya bayyana hakan ne, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a birnin Lagos. Masanin dai yana nazari ne kan alakar Sin da Afirka, ya kuma kware a fannin tattalin arziki da siyasar duniya.

Ya bayyana cewa, a 'yan shekarun da suka gabata, mahukuntan kasar Sin suna daukar managartan matakai game da raya kasar. Don haka, ya bukaci kasashe masu tasowa, musamman wadanda ke nahiyar Afirka,, da su koyi da ci gaban kasar Sin, domin raya kasashensu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China