Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kafafen yada labaran Afrika su taimakawa shirin AfCFTA
2019-10-05 15:42:03        cri

Hukumar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta MDD (ECA) ta bukaci 'yan jaridun kasashen Afrika da su taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar aiwatar da shirin yarjejeniyar ciniki maras shinge ta nahiyar Afrika wato AfCFTA, ta hanyar fadakar da al'ummar Afrika game da tasirin yarjejeniyar cinikin maras shinge ta Afrika.

Adeyinka Adeyemi, babban jami'in hukumar ta ECA, shi ne ya yi wannan kira, a yayin da yake bayyana muhimmiyar rawa da kafafen yada labarai za su taka wajen cimma nasarar aiwatar da shirin yarjejeniyar cinikin, musamman game da irin sauye sauyen da za ta haifarwa Afrika baki daya.

Adeyemi ya ce, kafafen yada labarai suna iya sauya tunanin jama'a ta hanyar gabatar da muhimman shirye shirye kan batun na AfCFTA domin fadakar da al'umma.

Ya kara da cewa, kafafen yada labarai suna da muhimmin nauyi dake bisa wuyasu wajen gabatar da wasu shirye shiryen wayar da kan al'umma game da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta hanyar shigar da al'ummar don a dama da su cikin ajandar shirin, ya ce hukumar ECA za ta samar da dukkan tallafin da ya dace wajen gabatar da shirin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China