Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Baje kolin Sin da kasashen Afirka ya fara haifar da sakamako
2019-07-19 19:50:41        cri

Sakatariyar kungiyar mata masu sana'ar hakar ma'adanai dake kasar Zambia Grace Njapau, ta yaba da irin nasarar da aka samu, sakamakon gudanar da bikin baje kolin hajojin Sin da na nahiyar Afirka da ya gudana a 'yan kwanakin baya.

Grace Njapau ta jinjinawa Sin bisa shirya taron, tana mai cewa, baje kolin ya haifar da damammaki na hadin gwiwa da zuba jari. Jami'ar ta yi wannan tsokaci ne yayin da take zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Juma'ar nan.

Ta ce baje kolin ya taimakawa Zambia, a fannin samun damar tallata hajojin ta, da ma cinikin su a sassan da suka shallake yankin ta. Kaza lika hakan ya kara kulla wata alaka mai nagarta, tsakanin 'yan kasuwar kasar da takwarorin su na sauran sassa, ciki hadda kungiyar matan.

Njapau ta kara da cewa, yanzu haka mambobin kungiyar su, sun hadu da karin abokan hulda da masu zuba jari, ciki hadda masu sana'ar hakar ma'adinai, da kamfanonin sarrafa kayan kwalliya na duwatsu masu daraja.

Daga nan sai ta yi kira ga matan Zambia, da su yi amfani da wannan dama da gwamnatocin Zambia da Sin suka samar, wajen bunkasa hada hadar hajojin kayan ado na duwatsun kasar masu daraja.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China