Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Zambia ta jaddada muhimmancin koyon Sinanci
2019-08-13 12:07:57        cri

Wata jami'ar gwamnatin Zambia, ta ce da yawa daga cikin matasan kasar na sha'awar koyon harshen Sinanci domin cike gibin fahimtar juna dake akwai tsakaninsu da Sinawa masu zuba jari.

Mary Chibesa, kwamishinar yankin Chingola, ta bayyana a jiya cewa, karuwar jarin Sinawa a Zambia, na bukatar al'ummar kasar su iya Sinanci domin saukaka matsalar bambamcin harshe.

Mary Chibesa ta ce shigar kamfanonin Sin yankin Chingola da ma kasar baki daya, na bukatar inganta mu'amala da su.

Ta ce sanya harshen Sinanci cikin manhajar karatu a makarantun kasar hanya ce da ta dace.

Mabvuto Phiri, matashin dan kasuwa a kasar, ya ce kasar Sin na hada hannu da kasashen Afrika wajen samar da ci gaba, musammam raya ababen more rayuwa, don haka, koyon Sinanci na da muhimmaci.

Ya ce ya kamata matasa su koyi harshen Sinanci idan suna son su kulla alakar kasuwanci da takwarorinsu na kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China