Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Malawi da bangarorin adawa sun shirya hawan teburin sulhu
2019-10-22 11:17:05        cri
Gwamnatin Malawi da bangaren adawa da kawancen masu rajin kare hakkin dan Adam HRDC, sun ce sun shirya hawa teburin sulhu domin kawo karshen rikicin kasar da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 21 ga watan Mayu.

Wannan na zuwa ne mako guda, bayan MDD da ofisoshin jakadanci 6 dake Malawi, sun yi tir da rikicin na bayan zabe a kasar, suna masu kira da a gaggauta hawa teburin sulhu tsakanin gwamnatin Malawi da da dukkan masu ruwa da tsaki, domin kawo karshen rikicin.

Kawo yanzu, rikicin bayan zaben ya yi sanadin mutuwar mutane 4 da lalata kadadrorin da darajarsu ta kai miliyoyin daloli.

Gwamnatin Malawi da 'yan adawa da kungiyar HRDC, sun shaidawa kafafen yada labaru na kasar cewa, sun shirya tattaunawa da nufin kawo karshen rikicin kasar kafin ya yi Kamari. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China