Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malawi ta mayarwa AU-SARO martani kan zargin da suka yi game da zaben kasar
2019-06-09 16:48:02        cri
Gwamnatin kasar Malawi ta ce ta yi matukar kaduwa game da zargin da kungiyar tarayyar Afrika reshen ofishin shiyyar kudanci na kungiyar wato (AU-SARO), inda suka yi zargin cewa 'yan sanda sun yi amfani da karfin da ya wuce kima kan fararen hula a lokacin rikicin bayan zaben kasar.

Bayan tashin hankalin da aka samu tsakanin 'yan sandan kasar ta Malawi da 'yan adawar jam'iyyar Congress ta Malawi, a Lilongwe a ranar Alhamis, inda 'yan sandan suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashen roba domin daidaita rikicin, AU-SARO ta zargin gwamnatin Malawi kana ta yi Allah wadai da daukar wannan matakin.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, AU-SARO, ta gargadin gwamnatin kasar Malawi inda ta ce daukar irin wannan matakin zai iya haifar da barkewar tashin hankalin da za'a gagara shawo kansa a yankin, kana matakin zai iya wargaza duk wasu matakan siyasa da na diflomasiyya a kasar.

Sai dai a jiya Asabar, gwamnatin Malawi ta yi watsi da zargin na AU-SARO, tana mai cewa, 'yan sandan Malawi suna gudanar da aikinsu ne bisa ka'idar aiki ba tare da wuce iyaka ba a duk lokacin da suke bakin aikinsu.

A sanarwar da aka rabawa manema labarai ta hannun ma'aikatar harkokin wajen kasar, gwamnatin kasar Malawi ta bukaci AU-SARO ta bi hanyar diflomasiyya mafi dacewa a yayin mu'amalarta da kasar Malawi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China