Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rantsar da sabon zababben shugaban kasar Malawi
2019-05-29 09:45:20        cri

Sabon zababben shugaban kasar Malawi Peter Mutharika, ya sha rantsuwar kama aiki a jiya Talata, domin fara zango na biyu kuma na karshe na jagorancin kasar sa.

Yayin bikin rantsuwar, shugaba Mutharika ya yi kira ga al'ummun kasar sa, da su hade kai waje guda domin cimma nasarar kudurorin da kasar ta sanya gaba.

Mutharika tare da mataimakin sa Everton Chimulirenji, sun sha rantsuwar kama aiki ne a gaban babban mai shari'ar kasar Andrew Nyirenda, yayin bikin da aka shirya a filin wasa na Kamuzu, bikin da ya samu halartar daruruwan magoya bayansa, da kuma shugaban kasar na biyu Bakili Muluzi.

Cikin jawabin nasa, shugaban ya ce "Yakin neman zabe ya kare. Ko shakka babu, akwai lokaci na yakin neman kuri'u, da na hade kai waje guda. Akwai lokacin jayayya, da kuma na yarda da juna. Akwai lokacin neman cimma muradun kai, da na sanya bukatun kasa gaban komai.

Daga nan sai ya yi kira ga jagororin kasar, da su karbi nasarar da ya samu a matsayin tasu, duba da cewa, mutum guda ne kadai ke iya zama shugaba. Ya kuma godewa al'ummar kasar bisa zabarsa da suka yi, yana mai cewa nasarar sa ta daukacin 'yan kasar ce, kana za ta taimaka wajen wanzar da bin doka da oda, da ingantar tsarin dimokaradiyyar kasar. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China