Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Peter Mutharika ya lashe zaben shugaban kasar Malawi
2019-05-28 10:09:28        cri
Sakamakon hukumar zabe ta kasar Malawi, ya ayyana shugaban kasar mai ci Peter Mutharika, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan ya samu kaso 38.57 na kuri'un da aka kada.

Shugaba Mutharika ya doke abokin hammayarsa Lazarus Chakwera na jam'iyyar MPC dake zaman babbar jam'iyyar adawa ta kasar da ya samu kaso 35.41 na kuri'un da aka kada, yayin da mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima, ya zo na 3 da kaso 20.24 na kuri'un, a wani takara mai zafi da aka yi a kasar.

Shugabar hukumar zabe ta kasar Mai shari'a Jane Ansah, wadda ta sanar da sakamakon, ta ce mutane miliyan 5.1 daga cikin miliyan 6.8 da suka yi rejista ne suka kada kuri'a a zaben, adadin da ya kama kaso 74.44 cikin 100 na mutanen da suka kada kuri'a.

Ta ce hukumar ta kuma bayyana dukkan korafe-korafen da jam'iyyu daban daban suka gabatar, tana mai cewa, an gudanar da sahihin zabe wanda kuma ya bayyana ainihin muradin kasar Malawi. (Fa'iza Mustapha)

 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China