Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya aike da sakon taya murna ga taron kamfanonin kasa da kasa karo na farko
2019-10-19 15:19:03        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taro karon farko na kamfanonin kasa da kasa na Qindao, da aka bude yau Asabar a lardin Qingdao dake gabashin kasar Sin.

A cewar shugaban Xi, a matsayinsu na wadanda aka dama da suka kuma shaida tare da cin gajiya, kamfanonin kasa da kasa sun taka muhimmiyar rawa cikin sama da shekaru 40 da kasar Sin ta dauka tana bin manufar bude kofa da gyare-gyare a gida.

Ya kara da cewa, kofofin kasar Sin za su ci gaba da budewa, sannan yanayin kasuwaci zai yi ta kyautatu, kuma damarmaki ga kamfanonin kasa da kasa, za su yi ta karuwa.

Har ila yau, shugaban ya ce kasar Sin na maraba da 'yan kasuwan kasashen duniya su zo su zuba jari tare da hada hannu a kokarin samun sakamako na moriyar juna da samar da kyakkyawar makoma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China