Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya rubuta wasikar taya murnar babban taron yanar gizo ta kasa da kasa karo na 6
2019-10-20 17:06:32        cri

An bude babban taron yanar gizo na kasa da kasa karo na 6 a Wuzhen na lardin Zhejiang na kasar Sin, inda shugaban kasar Xi Jinping ya rubuta wasika don taya murna.

A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 50 da aka soma amfani da yanar gizo. Yanzu haka, ana ta gaggauta yin kwaskwarima kan fannin kimiyya da fasaha da masana'antu na sabon zagaye, kana ana ta samun ci gaba wajen amfani da wasu sabbin fasahohi, ciki har da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, fasahar manyan alkaluma, abubuwan intanet da dai sauransu, gaskiya sana'ar yanar gizo na fuskantar makoma mafi kyau a nan gaba. Bunkasa da amfani da gudanar da harkokin yanar gizo, don sanya sana'ar ta kara samar da alheri ga dan Adam, wannan nauyin bai daya ne dake kan wuyan kasashen duniya.

Wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ta Sin, kuma shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al'umma na kwamitin tsakiya na JKS ta kasar Huang Kunming ya halarci bikin bude taron, inda ya karanta wannan wasikar taya murnar da Xi ya rubuta, tare da gabatar da muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Huang ya nuna cewa, manufar da shugaba Xi ya gabatar a cikin wasikar, ta nuna tunani mai zurfi da ya yi kan ci gaban fannin yanar gizo, da kulawar da yake nunawa kan moriyar bai daya ta bil Adama, kana da bayyana fatansa na sahihanci kan hada kai tare da kasashe daban daban da nufin kafa makomar bai daya a fannin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China