![]() |
|
2019-10-21 11:17:05 cri |
Xi Jinping, wanda kuma shi ne Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya ce duniya na fuskantar sauye-sauyen da aka dade ba a gani ba, kuma samar da zaman lafiya da hadin gwiwar moriyar juna abubuwa ne da ba za a iya kauce musu ba yayin da ake fuskantar sauye-sauyen, yana mai cewa da sauran tafiya wajen cimma ci gaba da tsaro na bai daya.
Xi ya yi wannan tsokaci ne cikin sakon taya murna da ya aike ga dandalin Xiangshan, taron tsaro na shekara-shekara da aka fara yau Litinin a nan birnin Beijing.
Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da kokarin wanzar da zaman lafiya da bada gudunmuwa ga ci gaban duniya da kuma kiyaye dokokin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China