Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin cinikin intanet Jumia na Najeriya ya nemi hadin gwiwa da Sin
2019-10-18 10:07:06        cri

Babban kamfanin hada hadar kasuwanci ta intanet na Najeriya wato Jumia yana neman kara yin hadin gwiwa da kasar Sin domin bunkasar harkokin kasuwancinsa, wani babban jami'in kamfanin ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Jeremy Doutte, mataimakin shugaban rukunin kamfanin na Jumia, ya bayyanawa Xinhua a Nairobi cewa, kamfanin nasa zai halarci taron karawa juna sani na kasa da kasa kan batun intanet karo na 6 wanda zai gudana tsakanin ranakun 20 zuwa 22 ga watan Oktoba a garin Wuzhen, dake lardin Zhejiang na kasar Sin, domin kara yin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin.

Doutte ya ce, sun ba da fifiko matuka ga taron na karawa juna sani saboda suna da burin zurfafa mu'amala da tsarin cinikin intanet na kasar Sin, ya kara da cewa, wannan shi ne karon farko da kamfanin Jumia zai halarci taron.

A hirarsa da Xinhua, Doutte ya ce, suna fatan za su kara gina muhimmiyar dangantakar kasuwanci da shugabannin duniya a fannin ciniki ta intanet, wanda ya kunshi kamfanonin kasar Sin, ya ce, kamfaninsu zai samu karin ilmi mai yawa daga tsarin ciniki ta intanet na kasar Sin wadda ta samu matukar ci gaba a wannan fanni.

Jumia, an kafa shi a shekarar 2012 a Najeriya, ya bude ofishinsa a birnin Shenzhen na kasar Sin dake gabar teku shekaru uku da suka wuce, ya fara aiki da ma'aikata biyu rak, amma daga wancan lokacin zuwa yanzu yana da ma'aikata kimanin 50 wadanda ke gudanar da ayyuka daban daban da suka hada da nemo manyan dillalai da za su shiga harkokin kasuwancin na zamani.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China