Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce an samu kyautatuwar tsaro
2019-09-20 20:00:10        cri

Rundunar 'yan sandan tarayyar Najeriya ta ce, a baya bayan nan, ana samun kyautatuwar tsaro a sassan kasar, idan an yi la'akari da alkaluman da rundunonin tsaron kasar suka tattara cikin watanni 3 da suka shude.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Alhamis, bayan wata ganawa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, babban sifeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu, ya ce ayyukan laifi kamar garkuwa da mutane, da fashi da makami, da sauran munanan laifuka sun ragu a kasar.

Kaza lika a cewar sa, ayyukan 'yan bindiga da suka dade suna addabar wasu sassa na arewacin kasar su ma sun ragu, idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a baya.

A jiya Alhamin din ne dai manyan jami'an rundunonin tsaron Najeriyar suka yi wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, inda suka tattauna lamurra da dama da suka jibanci tsaron kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China