Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Basine masanin kimiyya ya lashe lambar yabo a Najeriya
2019-09-05 10:40:42        cri

Wani Basine masanin kimiyya, tare da abokin aikinsa wani mai bincike dan Najeriya, sun yi nasarar lashe lambar yabo mafi daraja ta kasa a fannin kimiyya, bayan irin bajintar da suka nuna bisa gudumowar da suka bayar ga fannin ci gaban kimiyya da fasahar kirkire kirkire.

Hukumar ba da lambar yabo ta kasar ta fada a taron manema labarai cewa, Wang Meihong, da Mathew Aneke, sun lashe lambar yabo ta kimiyya ta wannan shekara, inda suka samu kyautar kudi dalar Amurka 100,000 bisa ayyukan da suka gudanar na hada wasu sinadarai, da tsirrai, wajen samar da makamashin lantarki.

A tarihin shekaru 15, wannan shi ne karon farko da wani mutum dan kasar waje ya samu lambar yabon, wanda kamfanin sarrafa iskar gas wato LNG na Najeriya ke daukar nauyi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China