Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya taya Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwarta
2019-10-02 15:50:31        cri

A jajibirin bikin kafuwar kasar Sin a ranar 1 ga wata, a madadin gwamnati da jama'ar tarayyar Najeriya, shugaban kasar Muhamadu Buhari ya aikawa babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping sakon taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, inda ya bayyana cewa, yayin da ake gudanar da wannan gagarumin biki mai ma'ana a tarihi, a madadin gwamnati da jama'ar Najeriya, yana taya shugaba Xi da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da Sinawa murna. A cikin shekaru 70 da suka gabata, jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta samu ci gaba cikin lumana har ta kawo alheri ga daukacin al'ummomin kasashen duniya, muna farin ciki matuka da ganin Sinawa masu himma da kwazo da kuma kishin kasa suna sanya kokarin neman samun ci gaban kasa a karkashin jagorancin shugabannin kasar Sin, kana dandalin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka ya samar da sabon dandalin raya kasa ga kasashen Afirka.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, yana martaba huldar abota dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin bisa tsarin da aka kafa dandalin, kuma yana farin ciki da ganin ci gaban da kasashen biyu wato Sin da Najeriya suka samu yayin da suke gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China