![]() |
|
2019-05-14 10:49:51 cri |
Kididdigar da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar a jiya, ta ce kimanin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta 360,000 aka sayar a cikin watanni 4 na farkon bana, adadin da ya karu da kaso 59.8 bisa dari a kan na makamancin lokaci na bara. Haka kuma, aikin kera motocin ma ya karu da kaso 58.5 bisa dari.
Bunkasar bangaren ya biyo bayan namijin kokarin da gwamnati ta yi na bunkasa kasuwarsa ta hanyar bada ragi da rangwamen haraji a kan sayen motocin domin rage gurbatar yanayi da inganta amfani da motoci masu amfani da makamshi mai tsafta. (Fa'izaMustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China