Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WFP: Mutum 1 cikin 9 a duniya na fama da matsananciyar yunwa
2019-10-16 10:32:12        cri

Jami'in shirin samar da abinci na MDD (WFP) ya sanar cewa, sama da mutane miliyan 800, wato mutum guda cikin mutane 9 a duniya ne ba su da sukunin samun ingantaccen abincin da suke bukata, ba ma kawai a matsayin na rana guda ba har ma sauran kwanaki na rayuwarsu baki daya.

Herve Verhoosel, kakakin shirin na WFP, ya bayyana hakan a taron manema labarai a jiya Talata gabanin bikin tunawa da ranar abinci ta duniya, wacce ta fado a 16 ga watan Oktoba, ya ce kusan kaso 60 bisa 100 na adadin mutanen miliyan 800 suna fama da matsananciyar yunwa sakamakon tashe tashen hankula da ya shafi kasashensu.

Daga cikin kasashen da matsalar karancin abincin ta fi muni sun hada da Yemen, jamhuriyar Kongo, Afghanistan, Habasha, Syria, Sudan, Sudan ta kudu da Najeriya.

Ya ce tilas ne shugabannin duniya su tashi tsaye wajen lalibo hanyoyin magance dukkan tashe tashen hankula kuma a samar da yanayin tattara kudaden ayyukan tallafin jin kan bil adama, ya ce galibi abin da aka gina shi a tsawon lokaci cikin dare daya sai a rusa shi.

A cewar Verhoosel, ga miliyoyin mutane a kasashen da yaki ya daidaita kamar kasashen da aka ambata, batun ranar abinci ta duniya wata ma'ana take da shi na daban.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China