Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WFP: DRC tana fama da matsalar yunwa mai muni
2019-07-03 13:49:49        cri

Hukumar shirin samar da abinci ta MDD WFP ta bayyana cewa, jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), ita ce kasa ta biyu mafi fama da matsalar yunwa a duniya bayan kasar Yemen, inda mutane miliyan 13 suke fama da matsalar karancin abinci, yayin da kimanin kananan yara miliyan biyar a kasar ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, WFP ta bayyana hakan a ranar Talata.

Kakakin hukumar WFP dake Geneva, Herve Verhoosel, ya bayyana hakan a taron MDD, ya ce hukumar ta riga ta kai matsayin koli a bisa ayyukan jin kai da take samarwa ga mutanen dake yankunan da ake fama da yawan tashe tashen hankula a arewaci da gabashin jamhuriyar Kongo.

Matakin ya biyo bayan barkewar sabon fadan kabilanci, lamarin da ya tilastawa dubban mutane kauracewa gidajensu.

Ya ce a yankin da aka samu bullar cutar annobar Ebola a lardin Ituri, an samu barkewar tashin hankali tsakanin kabilun yankin, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka kimanin 160 a 'yan makonnin da suka gabata.

Mafi yawan mutanen da tashin hankalin ya shafa sun shiga cikin yanayin rashin abinci mai gina jiki, kuma an sha tilasta musu kauracewa matsugunansu, kana suna neman mafaka a wasu cibiyoyi dake birane da kuma cikin dazuka, in ji WFP.

Verhoosel ya ce, tashin hankalin ya barke a lardin Ituri, daya daga cikin larduna biyu na jamhuriyar Kongo, inda annobar cutar Ebolar ta fi kamari, kawo yanzu, ta hallaka rayuka sama da 1,400.

Hukumar shirin samar da abinci WFP ta ce, ana kokarin dakile bazuwar kwayar cutar ta hanyar bayar da taimakon kayan abinci ga wadanda suka kamu da cutar, lamarin da ya taimaka wajen takaita barazanar yaduwar cutar a tsakanin al'umma.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China