Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AMISOM da kwamandojin Somalia za su kara hada hannu wajen gudanar da ayyuka
2019-07-09 09:43:59        cri

Kwamandojin shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika dake aiki a Somalia wato AMISOM, sun kammala taronsu na yini 3 a Mogadishu, inda suka yanke shawarar kara hada hannu da dakarun kasar wajen aiwatar da tsarin ficewar daga Somalia.

Karkashin tsarin, shirin na AU zai mika ragamar kiyaye tsaron kasar ga jami'an tsaronta, gabanin ficewar AMISOM din da ake sa rai a shekarar 2021.

Francisco Madeira, wakilin musammam na shugaban hukumar AU a Somalia, wanda kuma ya rufe taron, ya yabawa dakarun kasar bisa ayyukan da suka gudanar a baya-bayan nan na 'yantar da wasu yankunan dake Lower Shabelle.

Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan taron, Francisco Madeira, ya ce jajircewarsu ta nuna kasar na da niyyar samun ci gaba duk da kalubalen da take fuskanta, inda ya ce, aikin dakarun kasar na bukatar goyon baya.

Kwamandojin da takwarorinsu na Somalia, sun hadu a Mogadishu ne domin bitar ci gaban da aka samu wajen aiwatar da kunshin daftarin ayyukan shirin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China