Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahalarta taron sulhun Kamaru sun nemi a baiwa yankin renon Ingilishi 'yancin gashin kai don kawo karshen rikicin 'yan aware
2019-10-05 16:30:38        cri

Yankunan Kamaru masu magana da yaren Turanci dake fama da hare haren mayakan 'yan aware tun a shekarar 2017 sun bukaci a baiwa yankunan ikon gashin kai, mahalartar taron sulhun na kasar Kamaru ne suka gabatar da wannan kuduri a ranar Juma'a.

Kamata ya yi a bai wa yankunan matsayin musamman a tsarin rabon mukaman gwamnatin kasar, kana a rage karfin ikon hukumar dake rike da madafun ikon kasar, sannan a baiwa yankunan kananan hukumomi 'yancin gashin kai wajen tafiyar da harkokin kudadensu, Felix Mbayu, wakilin musamman a taron tattaunawar sulhun kasar Kamaru ne ya bayyana hakan.

Firaministan Kamaru Joseph Dion Ngute, wanda ya jagoranci rufe taron tattauanwar, ya ce bangarori daban daban na al'ummar Kamaru sun gabatar da shawarwari sama da 1,000.

Ya ce, za'a iya aiwatar da wadannan shawarwari da aka gabatar a lokacin taron tattaunawar na kwanaki biyar ne idan har an samu cikakken yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Ya sake jaddada mika bukatar neman zaman lafiya musamman ga mutanen da idanunsu suka rufe suke ta kokarin tayar da hankalin kasa da aikata ta'addanci. Don haka ya sake bukatarsu da su ajiye makamansu. Ngute ya bayyana hakan ga mahalarta taron tattaunawar.

Shugabannin 'yan awaren dake zaune a kasashen waje wadanda ba su halarci taron tattaunawar sulhun ba sun yi watsi da shawarwarin, inda suka bayyana cewa, shawarwarin ba su da amfani kuma tamkar wasan yara ne, sun sha alwashin ci gaba da kaddamar da hare-hare.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China