Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gano sabbin wurare masu ma'adanai 300 a Kamaru
2019-09-04 12:48:57        cri

Kimanin sabbin wurare masu ma'adanai 300 aka gano a jamhuriyar Kamaru a cikin shekaru biyar da suka shude, ministan ma'aikatar ma'adanai, masana'antu, da bunkasa fasaha na Kamaru Gabriel Dodo Ndoke, shi ne ya tabbatar da hakan

Ndoke ya ce, sabbin ma'adanan sun hada da zinare, zinc, rare earth, uranium, nickel rutile, da manganese, ya bayyana hakan ne a lokacin bikin baje kolin ma'adanai na kasa da kasa na shekarar 2019 na jamhuriyar Kamaru wato (CIMEC) a takaice, wanda aka gudanar daga ranar Litinin zuwa Laraba a Yaounde, babban birnin kasar.

Ya ce, baje kolin na CIMEC, yana da babbar ma'ana game da alfanun da za'a samu na gajere da matsakaicin zango daga bangaren masu zuba jari, za'a samu damar ne ta hanyar fara ayyukan hakar ma'adanan a kasar.

A cewar masu shirya bikin baje kolin, a wannan shekarar bikin zai karkata ne wajen janyo hankalin kamfanonin aikin hakar ma'adanan, tare da tattaunawa game da yadda za'a tinkari aikin. Mahalarta sama da 100 za su gabatar da sabbin fasahohinsu da kayayyakin aikinsu na kamfanonin hakar ma'adanan a lokacin bikin baje kolin na wuni uku.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China