Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe bikin baje kolin lambun shan iska na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Beijing
2019-10-10 10:00:48        cri

A daren jiya Laraba, aka rufe bikin baje kolin lambun shan iska na kasa da kasa na shekarar 2019 a yankin Yanqing dake karkarar birnin Beijing, inda firaministan kasar Li Keqiang ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi.

A cikin jawabinsa Li ya nuna cewa, bikin na wannan karo ya karbi mahalarta mafiya yawa a tarihi, wanda ya kasance wani kasaitaccen biki na tuntubar juna a fannin tsirrai, dake gaggauta mu'ammalar al'adu tsakanin kasa da kasa da kara tuntubar jama'ar kasa da kasa da hadin kai a wannan fanni. Tun lokacin da aka shiga sabon karni, yawan tsirrai da aka shuka a duk fadin duniya ya karu da kashi 5 cikin dari, Sin tana ba da taimako na rubu'i daga cikinsu. Sin za kuma ta juya hanyar samun bunkasuwarta cikin sauri, da yin amfani da karfin kirkire-kikire da kuma kara bullo da sabbin makamashi. Sannan da amfanawa jama'a ta hanyar kiyaye muhalli da yaki da ayyukan gurbata muhalli, da raya yanayin zaman rayuwar jama'a. Sin za ta nace ga ka'idar daukar nauyin baki daya tare da yin la'akari da banbance banbancen dake tsakanin bangarori, da bin ka'idar adalci da ka'idar sauke nauyin dake wuyanta gwargwadon karfinta, don aiwatar da yarjejeniyar Paris wadda ke shafar sauyin yanayi yadda ya kamata, kuma Sin za ta yi iyakacin kokari taimakawa sauran kasashe masu tasowa wajen raya tattalin arziki mai dorewa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China