Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka mutu a hadarin jirgin ruwa a Kamaru ya kai 18
2019-08-29 20:27:19        cri

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, mutane 18 ne suka mutu, bayan da wani jirgin ruwa da suke ciki ya nutse a gabar ruwan yankin kudu maso yammacin kasar.

A cewar gwamnan yankin Bernad Okaila Bilal, masuntan Najeriya sun yi nasarar ceto mutane 4, yayin da sojojin ruwan Kamaru suka ceto mutane 107, lokacin da jirgin ruwan mallakar kamfanin Achouka na kasar ta Kamaru ya nutse.

Sai dai tawagar masu aikin ceto na ci gaba da neman wadanda suka bace.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China