Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da Kim sun taya juna murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyyar kasashensu
2019-10-06 15:55:52        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa (DPRK), a yau Lahadi sun taya juna murnar cika shekaru 70 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Shugaba Xi ya ce, DPRK tana daga cikin kasashen duniya da kasar Sin ta kulla huldar diflomasiyya da su a karon farko, a cikin shekaru 70 da suka gabata, karkashin jagoranci da sadaukarwar shugabannin kasashen biyu, dangantakar abokantaka bisa al'ada tsakanin Sin da DPRK ta kasance abin alfahari a tsawon lokaci, ta kawo sauye sauye ga harkokin kasa da kasa, kana tana ci gaba da karfafuwa a tsawon lokaci, sannan dangantakar ta samu kyakkyawan tushe a zukatan jama'ar kasashen biyu.

Xi ya kara da cewa, kasashen biyu suna cin gajiyar dangantakar hadin gwiwa a tsakaninsu daga dukkan fannoni, matakin ba kawai ya amfanawa moriya da makomar kasashen biyu ba ne, har ma ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo kyakkyawan sauyi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar.

Da yake nuna yabo game da kafuwar huldar diflomsiyyar tsakanin DPRK da Sin, Kim ya bayyana cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, kasashen biyu da al'ummomin kasashen biyu sun yi hadin gwiwa cikin himma da kwazo da tsayawa tsayin daka wajen karewa da daga matsayin tsarin gurguzu, kuma sun kafa tarihi game da kyakkyawar abokantakar dake tsakaninsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China