Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya mika sakon gaisuwa na ranar tsoffi ta kasar Sin
2019-10-07 15:36:25        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wa tsoffin kasar fatan alheri a bikin Chongyang, wato ranar tsoffi ta kasar bisa kalandar gargajiya, wadda ta fado a yau Litinin.

Shugaba Xi ya mika gaisuwan ne cikin martanin da ya yi na wata wasika da wasu tsoffi 30 mazauna yankin Macao suka rubuta masa.

Tsoffin suna aiki ne a cibiyar kula da tsoffi da aka kafa a shekarar 2007, inda shugaba Xi ya ziyarta a watan Junairun 2009, a lokacin da yake mataimakin shugaban kasar Sin.

A martanin, shugaban ya ce tsoffin sun ga yadda aka yi nasarar tafiyar da 'kasa 1 mai tsarin mulki 2' a yankin Macao, kuma yana farin ciki da jajarcewarsu wajen kulawa da walwalar al'umma, bayan da suka yi ritaya.

Ya kuma bayyana fatan tsoffin za su bayyanawa matasan Macao labaran abubuwan da suka wakana kafin da bayan dawowar Macao babban yankin kasar Sin da kuma karfafa musu gwiwar ci gaba da kaunar babban yankin kasar Sin da Macao da kuma ba da gudumuwarsu ga dunkulewar yankin Guangdong da Hong Kong da Macao da ake kira Greater Bay, da kuma hada hannu tare wajen kara kyautata yankin Macao.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China