Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da Putin sun taya juna murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Rasha
2019-10-02 20:34:49        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, a yau Laraba sun taya juna murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A sakon taya murnar da ya aike, Xi ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta cimma kaiwa matsayin koli zuwa matakin dangantakar amincewa juna ta fuskar mutunta juna da yarda da juna, da yin hadin gwiwa da cudanya da juna, kana ta bayar da muhimmiyar gudunmowa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, da ma ci gaban duniyar baki daya.

A nasa bangaren, Putin ya ce, kasarsa ita ce kasa ta farko a duniya da ta amince da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin (PRC), kuma ita ce kasar da ta fara kulla huldar kut-da-kut da kasar Sin. Dangantakar Rasha da Sin ta cimma nasarar zama abin alfahari a tarihi, a cewar mista Putin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China