Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ba da umarnin fitar da mai daga runbum adana man kasar bayan hare-haren da aka kai kan kamfanin hakar man Saudiya
2019-09-16 09:18:16        cri
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka, ya ba da umarnin fitar da mai daga runbum adana man fetur din kasar na musamman, bayan hare-haren da aka kaiwa na'urorin hakar man kasar Saudiya.

Trump, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, harin da aka kaiwa kamfanin hakar man Saudiya, yana iya yin tasiri kan farashin mai a kasuwannin duniya. Ya ce, idan akwai bukata, ya dace a san yawan man da zai wadatar da kasuwa.

Ya kara da cewa, ya sanar da dukkan hukumomin da abin ya shafa, da su umarci bututan man da umurnin ya shafa a Texas da sauran jihohin dake kasar wajen fitar da mai ba tare da bata lokaci ba.

Sashen kula da alkaluman makamashi na Amurka ya nuna cewa, yawan man da kasar take hakowa a kowace rana ya kai kusan ganga miliyan 10, inda matsakaici ya kai ganga miliyan 9.85 a watan Agusta a kowace rana. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China