Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya yi Allah wadai da kalaman manajan Houston Rockets kan yankin Hong Kong
2019-10-07 16:10:53        cri

Karamin jakadan kasar Sin dake Houston, ya yi Allah wadai da kalamai marasa tushe da babban manajan kungiyar wasan kwallon kwandon Houston Rockets ta kasar Amurka Daryl Morey ya yi kan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Kakakin karamin ofishin jakadancin na kasar Sin ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, "Mun kadu matuka da kalamai marasa tushe da Daryl Morey ya yi kan yankin Hong Kong, kana mun bayyanawa kungiyar Houston Rockets bacin ranmu. Mun kuma bukaci manajan kungiyar da ya gyara kuskuren da ya yi, da ma daukar matakan da suka dace na magance tasirin hakan ka iya yi."

Sanarwar ta kara da cewa, kawo karshen tashin hankali da dawo da doka da oda, shi ne abin da dukkan bangarorin rayuwa na yankin suka cimma matsaya a kai.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, duk wani mai kishi, zai goyi bayan kokarin da yankin musamman na Hong Kong ke yi na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Mai kungiyar Houston Rockets Tilman Fertitta, ya mayar da martani a shafinsa na Tweeter cewa, kalaman Morey ba na kungiyar ba ce, kuma kungiyar ba ta siyasa ba ce.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China