Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabar majalisar wakilan Amurka ta sanar da fara bincike kan bukatar tsige shugaban kasar
2019-09-25 10:21:48        cri

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta sanar da fara gudanar da bincike a hukumance, kan bukatar tsige shugaban kasar Donald Trump, game da tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da shugaban Ukraine.

A jawabinta, bayan kammala wani taron sirri da 'yan jam'iyyar Democrats na majalisar, Nancy Pelosi, ta ce tana sanar da yunkurin majalisar na fara bincike kan bukatar tsige shugaban kasar.

Shugabar, ta ce za ta ba kwamitocin majalisar 6 umarnin fara bincike kan shugaban karkashin binciken tsigewa

Donald Trump ya mayar da martani nan take, bayan sanarwar Pelosi, inda ya bayyana matakin a matsayin "cin zarafin shugaban kasar".

Shugaban ya ce, 'yan jam'iyyar Democrats ba su ga rubutaccen bayanin kiran ba, yana mai cewa, matakin na tsige shi, bita da kulli ne. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China