![]() |
|
2019-09-05 10:58:37 cri |
Jagororin shiga tsakani a tattaunawar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, sun amince su dauki kwararan matakai na samar yanayin da ya dace don kara yin tattaunawa a watan Oktoba.
An cimma wannan yarjejeniyar ce, yayin wata zantawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, mamba a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS kana jagoran kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka ya yi da wakilin cinikayya na Amurka Robert Lighthizer da sakataren baitul malin Amurka Steven Mnuchin bisa gayyatarsu.
Haka kuma, bangarorin biyu sun amince sun gudanar da zagaye na 13 na tattaunawar tattalin arziki da ciniki na manyan jami'an kasashen biyu a farkon watan Oktoba a birnin Washington, za kuma su rika tuntubar juna kafin ganawar.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China