Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu gabatar da shiri ta harsuna daban daban na CMG sun nuna kwarewa wajen gabatar da shirin bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2019-10-06 16:40:15        cri

A ranar 1 ga watan Oktoba, aka yi bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin. A cikin kasar Sin da ma kasashen waje, an saurari muryoyin masu gabatar da shirin ta harsuna daban daban na babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG. 'Yan jaridun kasashen waje sun kalli bikin tare da sauraron muryar masu gabatar da shirin ta harsuna daban daban, dukkansu sun nuna yabo gare su da cewa, sun fada kamar 'yan asalin kasashe masu amfani da harsunan.

A wannan karo, CMG ya gabatar da shirin bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin ta harsunan waje 43, da yaren Sinanci guda 4, da yaren kananan kabilun kasar guda 5, yawansu ya fi yawa a tarihi.

A cikinsu, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da shirin kai tsaye ta Sinanci, da yaren Canton, da Turanci, da Rashanci, da Faransanci da sauran harsunan waje. Kuma gidan telebijin na kasa da kasa na kasar Sin wato CGTN ya yi amfani da harsunan waje 5 wato Turanci, da Faransanci, da Spanisanci, da Larabci, da Rashanci wajen gabatar da shirin a wannan karo kai tsaye. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China