Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar People's Daily ta wallafa bayanai uku don jinjina yadda CMG ya watsa labaran bikin cika shekaru 70 da kafuwar PRC kai tsaye
2019-10-03 16:51:27        cri

Jaridar People's Daily ta wallafa wasu bayanai guda uku a yau Alhamis 3 ga wata domin jinjinawa babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG kan yadda ya watsa shirye-shirye kai tsaye game da bikin cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin wato PRC.

A cikin bayani mai taken "Shirin talibiji mai matukar kayawarta", an yi hira da masu kallon TV da masu duba shafin intanet daga kamfanonin kimiyya da fasahar zamani da kafofin watsa labarai da jami'o'i da ma rundunonin soja, inda suke ganin cewa, yadda rukunin CMG ya watsa shirye-shiryen kai tsaye ta hanyar amfani da fasahar zamani ta 4K da tsarin sauti mai inganci da ke karade zauren kallon, sun ji kamar suna filin Tian'anmen, kuma su kalli yadda aka yi babban faretin soja da jerin gwanon jama'a masu ban mamaki. Sun kuma nuna godiya ga ma'aikatan CMG bisa kokarinsu, 'yan kallon fiye da miliyan dari ne a fadin duniya suka kalli shirye-shiryen ta talibijin.

Jaridar People's Daily ta wallafa wani rahoto mai taken "sabbin fasahohin da aka yi amfani da su karo na farko a yayin watsa shirye-shiryen bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kaasr Sin kai tsaye", na nuna cewa, an yi amfani da sabbin fasahohi shida a wannan karo. Wato an yi amfani da injin daga da kuma sauke na'urorin daukar bidiyo a yayin bikin, wanda ya kawar da tasirin da aka samu a sauran na'urorin daukar bidiyo da kuma kallon shugabannin a yayin bikin, hakan ya sa shirin nuna bikin kai tsaye zama mai inganci yadda ya kamata. An yi amfani da motoci masu dauke da na'urorin daukar bidiyo yayin faretin soja, hakan ya taimaka wajen daukar bidiyon yadda kungiyoyin sojojin dake faretin a lokaci guda. A wannan karo, an makala wasu na'urorin daukar bidiyo a jikin wata igiya a kusa da tsakiyar dandalin, hakan ya sanya tutar kasar Sin da kungiyoyin sojojin dake faretin da kuma babban ginin Tian'anmen a cikin shirin bidiyo a lokaci guda. A karon farko, an tanadi wani injin da aka dora na'urorin daukar bidiyo a cikin motar daukar bidiyo a yayin da shugaban kasar Sin yake duba faretin girmamawa da sojojin suka shirya masa. Kana karon farko, an ajiye na'urorin daukar bidiyo a kasa kusa da kusa. Hakazalika kuma, an yi nazari da inganta kwaikwayon tsari a wannan karo.

Jaridar People's Daily ta wallafa wani rahoto mai taken "Za a nuna wani fim game da gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin da CCTV ya dauka ta hanyar yin amfani da fasahar 4K da aka kuma yi bayani cikin harshen Canton a sinimomin dake babban yankin Guangdong-HK-Macao", inda aka bayyana cewa, yayin da aka murna bikin a ranar 1 ga wata, a karo na farko gidan rediyon muryar babban yankin Guangdong-HK-Macao ya nuna bikin kai tsaye tare da yin bayani cikin harshen Canton, lamarin da ya samu karbuwa matuka daga wajen masu sauraro a babban yankin. Kana za a nuna wani fim game da wannan bikin a sinimomin yankin Guangdong-HK-Macao, inda za a nuna hotunan bidiyo masu inganci ta hanyar yin amfani da fasahar 4K da kuma yin bayani cikin yaren Canton. Ana sa ran sinimomi sama da 80 dake babban yankin za su fara nuna fim din a mataki na farko, misali sinimomi sama da 20 na lardin Guangdong ciki har da Huamei da Xingmei, da sinimomin Broadway da MCL da Emperor na yankin Hong Kong da sinimar Yongle ta yankin Macao za su nuna wannan fim a cikin kwanaki masu zuwa.(Kande, Zainab, Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China