Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a nuna fim kan bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin a sinimomin yankin Guangdong-HK-Macao
2019-10-02 19:24:14        cri

Za a nuna fim mai taken "A daidai wannan lokaci: Gagarumin bikin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin" da CCTV ya dauka ta hanyar yin amfani da fasahar 4K da kuma yin bayani da yaren Canton a sinimomin dake babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao a cikin kwanaki masu zuwa, wannan ne karo na biyu da ake shirin nuna babban fim ta fasahar 4K tun bayan da aka fara amfani da fasahar 4K wajen watsa hotunan bidiyo kai tsaye kan bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin a ranar 1 ga wata a cikin sinimomin da yawansu ya kai 70 a fadin kasar Sin, bisa mataki na farko, za a nuna fim a cikin sinimomi 80 a babban yankin.

Yau Laraba babban rukunin gidajen rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG da ofishin cudanya na gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake wakilci a yankin musamman na Hong Kong da hukumar kula da fina-finai ta kasar sun kira taron ganawa da manema labarai a nan birnin Beijing cikin hadin gwiwa, inda mataimakin ministan ma'aikatar yada manufofin kasar Sin kuma shugaban CMG Shen Haixiong da mataimakin darektan ofishin cudanya na gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake wakilci a yankin musamman na Hong Kong Yang Jian da mataimakin shugaban hukumar kula da fina-finai ta kasar Li Guoqi da sauran shugabanni suka halarci taron tare kuma da sanar da kaddamar da nuna fim din.

An ce, sinimomi sama da 20 na lardin Guangdong ciki har da Huamei da Xingmei, da sinimomin Broadway da MCL da Emperor na yankin Hong Kong da sinimar Yongle ta yankin Macao su ma za su nuna wannan fim a cikin kwanaki masu zuwa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China