Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani jami'in agaji ya mutu yayin da wasu 5 suka bata sanadiyyar harin Boko Haram a Nijeriya
2019-07-20 15:46:27        cri

Kungiyar agaji ta kasa da kasa mai yaki da yunwa wato The Action Against Hunger, ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta guda da batar wasu 5, biyo bayan wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai arewa maso gabashin Nijeriya.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, kungiyar ta ce mayakan Boko Haram ne suka farwa jerin gwanon motocin ma'aikatanta na lafiya, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa garin Damasak dake jihar Borno na yankin arewa maso gabashin kasar.

Ta ce jami'in da ya mutu direba ne da mayakan suka harba a lokacin da suka kai hari kan motocin kungiyar 3.

Sanarwar ta kara da cewa, har yanzu ba a ga sauran direbobin 2 da ma'aikatan lafiya 3 ba.

Kungiyar ta ce ta yi matukar bakin ciki da aukuwar lamarin, tana mai cewa, ma'aikatan sun sadaukar da kansu wajen ba da agajin ceto rai ga daidaikun mutane da iyalai da rikicin a yankin arewa maso gabashin Nijeriya ya shafa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China