Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Kamaru 7 sun ji rauni a hadarin da suka gamu a yankin magana da Turanci
2019-08-16 13:09:00        cri

Kimanin sojojin kasar Kamaru 7 ne suka samu raunuka bayan da tankar yakinsu ta yi hadari da yammacin ranar Alhamis a kan hanyar garin Kumba dake shiyyar kudu maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan kasar biyu masu fama da rikici wadanda ake magana da yaren Turanci, jami'in 'yan sandan yankin ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sandan ya ce, wasu daga cikin sojojin sun samu munanan raunukan dake baranazar mutuwarsu yayin da wasu daga cikinsu suka samu kananan raunuka. Sai dai an garzaya da dukkansu asibiti domin yi musu magani.

Sojojin, dukkansu suna cikin manyan jami'an sojojin Kamaru ne, na rundunar sojojin musamman ta (BIR), yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa aiki a Mamfe, wani gari da aka yi amanna yana karkashin ikon mayakan 'yan awaren kasar yayin da suka gamu da hadarin.

Mayakan 'yan awaren sun bayyana cewa su ne suka yi sanadiyyar hadarin bayan da suka binne wasu ababen fashewa a karkashin kasa, sai dai sojojin sun masanta ikirarin 'yan awaren, suna mai cewa, rashin kyawun hanya ne ya haddasa hadarin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China