Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin Hong Kong ta haramta sanya abubuwan rufe fuska yayin zanga-zanga
2019-10-04 19:49:05        cri

A yau ne, gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta fito da wata doka dake haramta sanya abubuwan rufe fuska, a matsayin wani sabon mataki na kawo karshen tashin hankalin da ya dade yana addabar yankin.

Jagorar yankin Carrie Lam, ta shaidawa taron manema labarai cewa, gwamnati na fatan dokar da aka bullo da ita, karkashin dokokin gaggawa mai sunan dokar hana sanya abubuwan rufe fuska, za ta yi tasiri kan masu rufe fuskokinsu, masu zanga-zanga da tayar da husuma.

A cewarta, an sanya haramcin ne da nufin kawo karshen tashin hankali da dawo da doka da oda. Dokar za ta fara aiki da tsakar daren yau Jumma'a.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China