Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi kira da hada kai wajen yaki da matsalar cutar Ebola
2019-10-04 15:34:41        cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi kira ga kasashen nahiyar, da su karfafa hadin gwiwa a kan iyakokinsu wajen hana yaduwar kwayar cutar Ebola.

Kungiyar mai mambobin kasashe 55, ta hanyar cibiyoyin hana yaduwa da kandagarkin cututtuka na Afirka (Africa CDC), ta bayyana hakan ne cikin mujallar da take wallafawa lokaci-lokaci cewa, karfafa hadin gwiwa a kan iyakokin juna game da riga kafi da matakan mayar da martani kan kwayar cutar Ebola tsakanin Jamhuriyar Demokiradiyar Congo, yankin da cutar ta fi shafa da kasashen dake makwabtaka da ita, zai taimaka wajen hana yaduwar cutar zuwa sassan nahiyar.

Africa CDC, hukumar kungiyar da ta kware a fannin kiwon lafiya, ta sanar da cewa, za ta shirya wata ganawar ministocin lafiya na DRC da na kasashe 9 dake makwabtaka da ita, don tattauna matakan hadin gwiwa a kan iyakokin juna kan yaki da matsalar cutar Ebola.

Hukumar ta bayyana cewa, za a gudanar da wannan ganawa ce a ranar 21 ga watan Oktoba a Goma, babban birnin lardin arewacin Kivu na Jamhuriyar demokiradiyar Congo, an shirya taron ne bisa hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya. Ana kuma sa ran taron zai hallara abokan hulda na kasa da kasa.

A cewar AU, taron ministocin, zai kuma tattauna yadda za a aiwatar da hadin gwiwa a kan iyakokin kasashen, da yadda za a shirya da ma tuntukar barkewar kwayar cutar ta Ebola.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China