Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres Har yanzu cutar Ebola na zama babbar barazana a DRC
2019-09-03 09:57:35        cri

 

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, har yanzu cutar Ebola, na zama babbar barazanar lafiyar jama'a ga mazauna yankin arewa maso gabashin Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DR Congo) da ma kasar baki daya.

Jami'in na MDD, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ziyarci yankin Mangina dake lardin arewacin Kivu, inda aka fara ba da rahoton bullar cutar a shekarar da ta gabata.

Ya ce, akwai bukatar hada karfi da karfe a fannoni daban-daban, ciki har da bangaren tsaro. Idan kuma ana fatan ganin bayan wannan cuta, ya kamata a samu 'yancin yin zirga-zirga da damar shiga wuraren da ake da damuwa, da ma batun tsaro.

Guterres ya ce, wajibi ne MDD, mahukuntan kasar da ragowar kasa da kasa, su samar da abubuwan da ake bukata don ganin bayan wannan cuta. Haka kuma wajibi ne al'ummar Congo su fahimce cewa, dole a magance cututtuka kamar Malaria da kwalara, kamar yadda aka ga bayan cutar kyanda.

Sakataren na MDD ya tuna cewa, cututtukan kyanda da malariya, sun halaka mutane da dama a DRC fiye da cutar Ebola kanta, ko da yake Ebola ta haifar da karin babbar barazana a matakan kasa da na shiyya.

Bugu da kari, ya bukaci al'ummomin kasashen duniya, da su kara hada kai, wadanda tuni suka amsa kiran da aka yi na tara kudade don yakar cutar.

A ranar Asabar din da ta gabata ce dai, Mr Guterres ya isa birnin Goma, kana ya kammala rangadin nasa jiya Litinin a Kinshasa, inda ya gana da shugaba Felix Tshisekedi da firaministan kasar Sylvestre Ilunga da 'yan majalisun dokoki da wakilan 'yan adawan kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China