Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun yi arangama da mayakan Boko Haram
2019-07-19 20:29:03        cri

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun yi arangama da mayakan kungiyar Boko Haram a ranar Laraba, lamarin da ya kai ga hallaka mayakan Boko Harma 11, da kuma sojoji 5.

Rundunar ta ce mayakan Boko Haram sun yiwa dakarun ta kwantan bauna, a kusa da Jakana dake karamar hukumar Kaga ta jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya haifar da dauki ba dadi na tsawon mintuna kusan 20.

Babban hafsan dake jagorantar runduna mai yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a yankin manjo janar Bulama Biu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Maiduguri cewa, manyan sojoji 2, da kuma wasu jami'an rundunar 3 sun rasu yayin dauki ba dadin.

Biu ya ce bayan dan lokaci ana fafatawar, 'yan ta'addan sun tsere sakamakon ruwan wuta da suka sha daga dakarun soji.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China