![]() |
|
2019-07-18 19:44:58 cri |
A kalla manoma 6 ne aka tabbatar sun rasu, sakamakon wani hari da wasu mahara da ake tsammanin mayakan Boko Haram ne suka kaddamar, a yankin Muna Dalti, mai nisan kilomita 6 daga birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni daga rundunar sojojin kasar sun nuna cewa, an hallaka manoman ne a ranar Laraba, lokacin da 'yan bindigar suka aukawa yankin, suna tsaka da aiki a gonakin su. Majiyar rundunar sojojin ta ce mayakan na Boko Haram, sun kutsa kai cikin yankin ne a kan babura.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban dakarun dake tallafawa ayyukan yaki da kungiyar ta Boko Haram ko Civilian JTF a takaice Sheriff Danfulani, ya nuna matukar damuwa, game da yadda 'yan ta'addan suka samu damar kaiwa wannan yanki hari har karo biyu a baya.
Danfulani ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a lokutan baya, mayakan na Boko Haram, sun yi awon gaba da abinci da dabbobin da suka kwashewa manoman.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China