Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi maraba da sake dawo da tattaunawa tsakanin DPRK da Amurka
2019-10-03 15:24:47        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasarta, ta yi maraba da sanarwar da kasashen Koriya ta Arewa da Amurka suka bayar ta sake dawo da tattaunawa a tsakaninsu.

Madam Hua ta ce, kasar Sin na fatan sassan biyu za su yi amfani da wannan dama wajen samun kyakkyawan sakamako.

Hua wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya da dare, ta ce, kasar Sin tana maraba da sanarwar dawo da tattaunawa da tuntubar juna da kasashen biyu suka bayar.

Ta ce, har kullum kasar Sin tana goyon bayan tattaunawa tsakanin DPRK da Amurka da ma amfani da matakai na siyasa wajen warware batun zirin Koriya.

A ranar Talata ce, mataimakin ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa na farko Choe Son Hui, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kasarsa da Amurka sun amince su tuntubi juna a ranar 4 ga watan Oktoba, kana manyan jami'an kasashe za su tattauna a ranar 5 ga watan na Oktoba. Bayanai na cewa, bangaren Amurka ya tabbatar da wannan batu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China