2019-07-01 10:06:34 cri |
Mai magana da yawun Guterres, Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce, Antonio Guterres ya yi maraba da yadda shugabannin Amurka da Koriya suka gana a kauyen Panmunjom, musamman sanarwar cewa, Koriya ta arewa da Amurka za su sake dawo da tattaunawa a tsakaninsu.
Ya ce, babban sakataren yana goyon bayan kokarin da sassan biyu ke yi, na kulla sabuwar alakar wanzar da zaman lafiya mai dorewa, da tsaro da ma kawar da makaman nukiliya kwata-kwata daga zirin Koriya.
An ruwaito shugaba Donald Trump na Amurka a jiya Lahadi yana cewa, wasu tawagogi daga kasashen Amurka da Koriya ta rewa, za su fara ganawa " nan da makonni biyu ko uku" inda za su tattauna kan shirin nukiliyar kasar Koriya ta arewa, amma ya ce, ba ya gaggawar cimma yarjejeniya.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China