Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya karrama mahalarta bikin faretin sojojin ranar 'yancin kasa
2019-10-02 16:28:14        cri

A jiya Talata shugaban kwamitin aikin soja na kasar Sin, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanya hannu kan umurnin ba da lambobin yabo ga mahalarta gagarumin bikin faretin sojojin kasar wanda ya gudanar a tsakiyar Beijing, fadar mulkin kasar domin shagulgulan tunawa da cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Dakarun sojojin da suka halarci faretin sun nanata matsayar rundunar sojojin kasar Sin na ci gaba da yin biyayya ga umarnin jam'iyyar kwaminis a ko da yaushe, da kuma bayyana irin nasarorin da kasar ta cimma wajen karfafa tsaron kasa da karfin soji a cikin sabon zamanin da muke ciki.

Haka zalika, dakarun sun nuna aniyar rundunar sojojin kasar a ko da yaushe wajen nuna kwarewar aiki don tabbatar da ikon mallakar kasa, da tsaron kasa, da muradun ci gaban kasa, abu mafi muhimmanci shi ne kokarin cusawa jama'ar kasar Sin kishin kasarsu da karfafa musu gwiwa, a cewar umurnin kwamitin aikin sojan kasar.

Rundunar sojojin Sin ta yi kira ga dukkan sojojin kasar da su koyi sojojin kasar da suka halarci faretin, kana su sadaukar da kansu wajen gina wani tsarin rundunar soji mafi inganci a duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China