Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#China70#Shugabanni da jama'ar kasar Sin sun kalli bikin murnar cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin
2019-10-01 21:08:31        cri
A daren yau Talata, bisa agogon Beijing na kasar Sin ne, aka shirya bikin raye-raye da kide-kide a filin Tian'anmen dake tsakiyar birnin, a wani bangare na shagulgulan murnar cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran manyan kusoshin kasar, suka hau ginin Tian'anmen, don kallon bikin gami da taya jama'a murnar wannan rana.

Za a kwashe minti 90 ana gudanar da bikin, inda za a nuna raye-raye da kide-kide, gami da nune-nunen wasan wuta, da dai sauransu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China