Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban bankin Nijeriya ya ce akwai damarmakin kasuwanci a bangaren noma na kasar
2019-09-21 15:38:36        cri

Shugaban babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya ce akwai gagarumar damar bunkasa tattalin arziki a bangaren ayyukan noma na kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, Godwin Emefiele ya ce akwai damarmaki a bangaren kiwon kifi, inda ya ce a yanzu, yawan kifin da ake samarwa a kasar ya tsaya kan ton miliyan 0.8 yayin da bukatar kifin ya tsaya kan ton miliyan 2.7, wanda ya samar da gibin ton miliyan 1.9.

Ya ce yanzu shirin bankin shi ne, hada hannu da gwamnonin jihohin dake yankunan teku domin su raya sana'ar kiwon kifi, da nufin cike gibin na ton miliyan 1.9 tare kuma da kawo karshen dimbin kudin da ake kashewa na shigar da kifi daga kasashen waje.

A cewarsa, wannan gagarumar dama ce ta bunkasa tattalin arzikin jihohin ta hanyar samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari.

Har ila yau, ya ce an samu sauyi a bangaren noman auduga, kuma domin cimma sauyin, shirin bankin zai kunshi manoma 300,000 a jihohi 26 daga cikin 36 na kasar, a cikin wasu 'yan shekaru masu zuwa.

Domin farfado da bangaren masana'antar sarrafa auduga da masaku da samar da sutura, bankin ya sa ido kan noman kadada 200,000 na ingantaccen auduga da aka rabawa manoma 200,000 a fadin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China